Kwamitin da Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kafa domin tantance jiragen saman da za su yi jigilar Alhazan Najeriya ta fara aikin tantance kamfanonin jirage a Abuja.
Kakakin Hukumar NAHCON Fatima Usara ce ta sanar da haka inda ta kara da cewa hukumar ta zabo mambobin kwamitin ne daga hukumar NAHCON, hukumomin yaki da cin haci da rashawa, kwastam, hukumar jiragen sama da hukumar kula da jin dadin Alhazai na jihohi
Shugaban NAHCON Abdullahi Muhammad ya yi kira ga kwamitin da ta mai da hankali wajen gudanar da aiyukkan ta cewa duka abin da suka zaba shine za su yi amfani da kuma su duba irin yawan dubban alhazan da za su yi wa aiki.
A karshe Usara ta ce bana kamfanin jiragen sama bakwai ne suka nemi wannan aiki da NAHCON sannan ta yi kira ga kamfannonin da za a zaba su tabbata sun gudanar da aiyukkan su yadda ya kamata.