Shugaban Kungiyar neman kafa Biafra, Nnamdin Kanu ya yi ikirarin cewa dan takarar shgaban kasa Atiku Abubakar, bad an Najeriya ba ne, dan asalin kasa Kamaru ne.
“Kun san cewa kuwa Atiku Abubakar dan kasar Kamaru ne kuwa. Asalin yankin da aka haife shi a kasar Kamaru ya ke.” Haka Kanu ya bayyana a hirar kai-tsaye da aka yi da shi a gidan Radiyon Biafra ranar Asabar da karfe 6 na yamma.
Wannan furuci da Kanu ya yi ya kawo cece-ku-ce a soshiyar midiya.
Dalili kenan PREMIUM TIMES ta gudanar da binciken kwakwaf domin tabbatar da ikirarin da Kanu ya yi ko kuma akasin haka.
An haifi Atiku a garin Jada, wanda a baya ya na karkashin Karamar Hukumar Ganye ne ta Jihar Adamawa.
Ganye nan ne cibiyar kabilar Chamba.
A cikin 1961 ne a watan Fabrairu, aka hade wani yanki na Kamaru da Najeriya, bayan an gudanar da zaben jin ra’ayoyin jama’a, domin a ji idan su na so a hade su da Najeriya.
An damka yankin ne a karkashin kulawar Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a cikin 1919 a yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka rattaba hannu da kuma wadda aka jaddada cikinn1946, bayan kafa Kungiyar Majalisar Dinkin Duniya.
Ranar 1 Ga Oktoba 1961 aka maida Arwacin Kamaru zuwa Najeriya, ita kuma Kudancin Kamaru zuwa kasar Kamaru.
Ganye a wancan lokacin nan ne hedikwatar Kamaru ta Birtaniya, wadda aka hade da Najeriya.
Asalain Jada daga wancan yanki ne, kamar yadda Kanu ya fada, dama kwa ya san wannan a tarihance.
Sai dai kuma ya kamata a sani cewa an haifi Atiku a ranar 25 Nuwamba, 1946, kuma mahaifinn sa Garba, Bafulatani ne.
Don haka koma ta wacecfuska za a kalli Atiku, cikakken dan Najeriya ne.
Discussion about this post