Buhari ya lashe Kananan Hukumomi 12 da aka lissafa na Katsina,

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya na kan gaban Atiku Abubakar na PDP a dukkan Kananan Hukumomi 12 da aka lissafa sakamakon su a jiya Lahadi da dare.

Kananan Hukumomin kuwa sun hada da Danmusa, Safana, Dutsi, Batsari, Kusada da kuma Bakori.

Sauran wadanda aka lissafa tun da farko kuwa su ne Daura, Matasau, Ingawa, Kurfi, Sandamu da Rimi.

A Danmusa, APC 30,011, PDP kuma 7528.

A Safana APC na da 26631, PDP KUMA 5756.

A Dutsi APC 22583, PDP kuma 5330.

Batsari PDP ta ci 7916, APC kuma 26,774.

A Kusada APC ta samu 21,071, PDP kuma 6713.

Bakori APC ta samu 53,623, ita kuwa PDP 11,931.

Jihar Katsina na da kananan hukumomi 34. An fadi sakamakon 12, saura 24.

Share.

game da Author