MAGE MAI RAI TARA: Dino Melaye ya kada Smart a zaben Kogi

0

Sanata Dino Melaye na jam’iyyar PDP ya yi nasarar sake cin kujerar sa ta sanatan Kogi ta Yamma a jihar Kogi.

Jami’in INEC mai sanar da sakamakon zabe, Emmanuel Bala, ya ce Melaye ya ci kuri’u sama da dan takarar APC Smart Adeyemi.

Dino ya samu 85,395, shi kuma Adeyemi ya samu 66,901.

Dan takarar jam’iyyar ADC ne ya zo na uku da kuri’u 6861.

Dama kuma tun a jiya Lahadi sai da muka ruwaito cewa Dino Melaye ne a kan gaba a iyar kuri’un da aka lissafa.

Share.

game da Author