Jam’iyyar APC ce ta sanu nasar zaben shugaban kasa a jihar Bauchi. Ta samu kuri’u 798,428, ita kuma PDP ta samu kuri’u 209, 313.
Ya bayyana haka ne bayan da INEC ta kammala tattara dukkan kuri’un da aka jefa a Kananan Hukumomi 20 da ke fadin jihar.
Ya ce an yi wa mutane 2,453,512 rajista a jihar Bauchi, amma kuri’a milyan 1,075,330 kadai aka jefa.
A cikin su ne Buhari ya samu 798,512, PDP kuma ta samu 209,313.
Sai dai kuma ya bayyana cewa an samu kuri’un da ba a jefa kan ka’ida ba, da suka lalace har sama da 37,000.