Jami’in INEC ya zargi Sojoji da hargitsa zabe a Ribas

0

Jami’an zabe na Kananan Hukumomin Okrika da Ahoada da ke cikin jihar Ribas, sun zargi sojojin Najeriya da laifin dagula zabe a kananan hukumomin biyu.

Jami’an su uku, wato Emavworan Efeturi, Leo Okon da kuma Emotion Niki, sun je cibiyar tattara sakamakon zabe a cikin daren jiya Litinin.

Su ukun sun bayyana a gaban jama’a cewa babu wani ko wata hujja da za a iya cewa an yi zabe a yankunan na su.

Okon da Efeturi sun ce sojoji ne daga barikin 6 Division daga Fatakwal su ke da laifin tarwatsa zaben a Okrika.

Sun ci gaba da cewa sun kuma nemi jami’in sun a INEC mai alhakin tattara kuri’a, amma sun rasa inda ya shiga.

Okon wanda shi ne jami’in zabe a Okrika, ya yi zargin cewa wani soja mai suna Kaftin Inuwa ne kutso kai cikin ofishin tattara kuri’un, kuma tilasta a dakarar da tattara kuri’un.

Daga nan sai kuma suka kori kowa daga cikin ofishin tattara kuri’un, su k ace kowa ya fice.

Dangane da abin da ya faru a karamar hukumar Ahoada ta Yamma kuwa, ‘yan dabar APC da na PDP ne su ka rika yin harbin kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya sa aka kasa samun damar tattara sakamakon zabe. Haka Niki ya shaida, wanda shi ma jami’in zabe ne.

Dalilin haka ne suka ce ba a samu damar tattara sahihin sakamakon zabe a wadannan yankuna uku ba.

Akalla an rasa mutane 11 ciki har da soja daya a rikicin zaben Jihar Ribas.

Yayin da sojoji suka ce magoya bayan PDP ne suka tayar da rikici, wata sanarwa kuma daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas ta ce Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ne ya za zugar sojoji 100 daga barikin 6 Division, suka mamaye ofishin INEC inda ake tattara zabe a Karamar Hukumar Isiokpo.

Share.

game da Author