A ra’ayi na da Buhari ya sa hannu a Kudirin Gyaran Dokar Zabe – Inji El-Rufai

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa da Shugaba Muhammadu Buhari ya sani, to da ya sa wa Sabon Kudirin Dokar Zabe Hannu.

El-Rufai ya yi wannan kalami ne a cikin wata hira da ya yi da Gidan Talbijin na Channels a makonni da suka wuce.

Gwamnan ya ce ya yi nazarin Sabon Kudirin Gyaran Dokar Zabe sosai, amma abin da ya fahimta, shi ne babu wani takamaimen abin da ya sauya sabon kudirin dokar daga Dokar Zabe ta ainihi.

“Don haka sai na raya a raina cewa, shin ya kamata Shugaban Kasa ya sa wa sabon kudirin dokar hannu kuwa? Sai na bai wa kaina amsa cewa, kamata ya yi da ya saka hannu kawai.

“Amma fa wannan ne ra’ayi na kafin ya yanke shawarar kin sanya hannu a sabon gyararren kudirin, wanda ya nemi canja salo da fasalin zaben gaba daya.”

“Amma ina daga cikin wadanda daga bisani suka ce kada a sanya wa dokar hannu, saboda akwai wani tuggu a cikin Sabon Kudirin Dokar Zaben, wanda ba zai yi wa al’ummar kasar nan dadi ba. Kuma daga Majalisar Tarayya aka shirya ajandar a cikin Sabon Kudirin.

“Saboda kwata-kwata ya rabauta daga wancan na farko da aka mika wa Shugaban Kasa, wanda ba shi da wani bambanci da ainihin Dokar Zabe.”

Gwamnan na Kaduna ya ce don Shugaban Kasa bai sa hannu a sabon kudirin dokar ba, hakan ba zai hana INEC tattara bayanan sakamakon zabe ta intanet ba, domin ita dokar zabe abu ce da za a iya fadada ma’anar ta.

Ya ce INEC za ta iya tattara bayanan sakamakon zabe ta hanyar intanet idan ta fadada ma’anar karfin ikon da Dokar Zabe ta bai wa hukumar.

Share.

game da Author