Buhari ya cancanci yabo – Dan Sule Lamido

0

Dan takarar Sanatan Jigawa ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP, Mustafa Sule Lamido, ya bayyana cewa ya samu karin karfin guiwar fitowa takara dalilin shigo da dokar da ta karfafa wa matasa fitowa takara da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ne.

Mustafa wanda da ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon dan takarar shugabancin kasa a karkashin PDP, ya yi wannan bayani jiya Alhamis a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce shigo da dokar ya yi fa’ida domin da a ce na a shigo da dokar ba, to da bai samu kwarin guiwar fitowa takarar ta sanata ba.

Ya jinjina wa Majalisar Tarayya saboda shigo da dokar da kuma goya mata baya da suka yi.

Mustafa ya ce ya na da yakinin samun nasara, saboda abin da ya kira rashin kyakkyawan wakilci da sanatan APC da ke kai, Sabo Nakudu ke yi wa shiyyar mazabar sa.

Mahaifin sa Sule ne jigon siyasar PDP a Jigawa, kuma ya na goya wa Atiku Abubakar baya domin ganin cewa PDP ta yi nasara a Jigawa da kasa baki daya.

Share.

game da Author