An yi wa El-Rufai Goma ta Arziki a Zaria da Sabongari

0

Dubban magoya baya ne suka yi tururuwa zuwa wajen tarban gwamnan jihar Kaduna Mal Nasir El-Rufai da tawagar sa a ziyara da suka kai garin Zaria da Sabongari domin Kamfen.

Wannan taro dai yayi taro domin masoyan gwamna Nasir da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC duk sun halarci garin Zaria da Sabongari.

A jawabinsa gwamna El-Rufai ya yabawa mutanen kananan hukumomin sannan ya bayyana cewa gwamnatin sa ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta ci gaba da malala wa mutanen yankin da jihar Kaduna romon dimokradiyya.

El-Rufai ya kara da yin kira ga mutanen yankin da su bashi dama a karo na biyu domin ci gaba da kyawawan ayyukan da ya ke yi a jihar.

Bayan kammala ziyararsa a garin Zaria, El-Rufai ya garzaya zuwa karamar hukumar Sabongari inda a nan ma ya yi kicibus da dandazon masoya da magoya baya. A garin Sabongari El-Rufai ya jinjina wa mutanen yankin sannan ya yi alkawari ci gaba da ayyuka kamar yadda ya riga ya fara.

Ya yaba musu bisa goyon bayan da suka rika bashi tun hawan sa mulkin Kaduna.

Share.

game da Author