‘Yan sanda ba za su cusa kan su a siyasa ba, za mu yi aiki kamar yadda doka ta gindaya – Inji Sufeto Adamu

0

Sabon shugaban rundunar ‘Yan sandan Najeriya, Sufeto Adamu Abubakar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa a karkashin sa ba zai zuba ida ba ya bari jami’an ‘yan sanda sa su rika cusa kan su a siyasa.

Adamu ya bayyana cewa a karkashin sa ‘yan sanda za su yi aiki ne kamar yadda doka ta shimfida.

” Ina so in sanar muku cewa a karkashina ba zan bari wani jami’in dan sanda na cusa kan sa a siyasa ba, Za mu yi aiki ne kamar yadda dokar kasa ta gindaya. sannan kuma zamu tabbatta mun yi abin da ya kamata ne ba don wai ko don mu burge ba ko kuma mu nuna fifiko ga wani bangare.

Adamu ya godewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa wnada shi shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya din da yayi. Ya ce zai maida hankali wajen ganin ya dawo da martabar jami’an ‘yan sanda a idanun mutanen kasar nan.

” Abin da zamu maida hankali a kai shine maganan yin garkuwa da mutane da ake yi a kasar nan da ayyukan ta’addanci. Za mu canza salo wajen tunkarar su da ganin an samu nasara akan haka.

Sufeto Adamu ya maye gurbin Idris Ibrahim ne da ya yi murabus a yau Talata.

Share.

game da Author