Gobara ta lashe kayayyaki na miyoyin nairori a jihar Zamfara

0

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Zamfara ta ce gobara ta lashe kayayyaki na milyoyin nairori a jihar a farkon wannan wata na Janairu.

Shugaban hukumar Sanusi Kwatarkwashi ne ya bayyana haka yau Talata a Gusau, babban birnin Jihar.

Ya ce gobarar ta faru ne a ranakun 11 da 12 Ga Janairu.

Gobara ta farko ya ce ta tashi ne a gidan Nuhu Anka, wanda shi ne Manajan Darakta na Gidajen Radiyo da Talbijin na Jihar Zamfara, sai kuwa wadda ta tashi washegari a gidan Hadi Sulaiman, Babban Sakatare na Hukumar Karatun Al’kur’ani da Tajawidi.

Ya ce gidan farko wutar ta ci kayayyaki sun kai na milyan 11, yayin da gida na biyu kuma na yi asara za ta kai ta naira miliyan 7.

Share.

game da Author