Kamfanin Dangote Industries Limited ya musanta cewa motar kamfanin sa ce ta kashe motane a garin Iworoko na jihar Ekiti.
A cikin wata takarda da kamfanin ya fitar jiya Lahadi, ya ce ba gaskiya ba ne rahotannin da wasu kafafe suka watsa cewa motar Dangote ce dauke da lodin shinkafa, wadda ta kashe jama’a a shekaranjiya Asabar da rana a garin.
“Dangote Industries Limited (DIL) ba ya shigo da shinkafa domin sayar da ita a kasuwa, ko wani ko wasu gungun jama’a.
Haka kuma motocin Dangote ba su dauko wa wani wanda ba a umarce su ba kaya. Kuma mun sha shaida wa jama’a cewa su rika kawo rahoton duk wata mota da aka ga ta dauko dakon wasu kayan da ba a ce ya dauko ba. idan an tuna, har lada ma mu ka ce za mu rika bayarwa.”
Kamfanin na Dangote ya ci gaba da cewa ya na da motocin tirela kamar 10,000 a Najeriya da cikin sauran kasashen Afrika ta Yamma.
Ya kuma lissafa kayayyakin kamfanonin Dangote da aka ce su kadai aka amince su rika dauka.
Kayayyakin sun hada da na: Dangote Cement Plc – Dangote Cement, Limestone, High-Grade Gypsum, and Coal; Dangote Sugar Refinery Plc- Dangote Sugar; NASCON Allied Industries Plc – Dangote Salt & DanQ Seasoning; Agro sacks Industries Limited – Bags; Dangote Flour Mills Plc – (Dangote Wheat, Flour da kuma Danvita).
Dangote industries Limited ya kuma nuna jimami da ta’aziyyar wadanda suka rasu sanadiyyar hatsarin.