Kwararan dalilan da ya sa bai kamata ‘yan Najeriya su sake zaben Buhari ba – Saraki

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana abin da ya kira kwararan dalilan da ya ce su ne hujjar da zai iya kafawa cewa bai kamata ‘yan Najeriya su sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu ba.

Da ya ke tattaunawa a Gidan Talbijin na Channels, cikin wata doguwar hira da aka yi da shi, Saraki yayi maganganu masu zafi a matsayin sa na Darktan Yakin neman zaben shugaban kasa na Atiku Abubakar, a karkashin jam’iyyar PDP.

BATUN GABATOWAR KAMFEN

Saraki ya bayyana cewa idan aka lura, tun farkon gabatowar kamfen, za a ga kungiyoyin sa-ido da masu kare hakkin dan adam sun fara dari-dari da wannan gwamnatin, musamman ganin yadda gwamnati ke kokarin karya fuka-fikin masu fadar albarkacin bakin su.

Bukola ya kara da cewa ya na magana ne a kan yadda gwamnatin Buhari ta ki bari a yi yakin neman zabe kamar yadda aka saba yi, kamar yadda ya kamara a yi. Ya na nufin a bar kowa ya goyi bayan duk wanda ra’ayin sa ke so.

“Ka ga a baya za ka ga ana yin taron hada gidauniyar gudummawar kudin kamfen da manyan ‘yan kasuwa, kuma ana taruka daban-daban. Amma yanzu wadannan manyan ‘yan kasuwa su na ta janye jikin su daga shiga cikin sha’anin siyasa.

“Amma duk da barazana da takure mu da takure kamfen din mu, wannan bai zai hana mu isar da sakon mu ga jama’a ba, domin mu na ci gaba da yin haka din, kuma ana fahimtar mu, mu na kuma kara samun goyon baya.

Ya buga misali da cea akwai kungiyoyin sa-kai da dama wadanda a baya su na da ‘yancin fitowa su fadi albarkacin bakin su. A tanzu kuwa ya ce kowa kaffa-kaffa ya ke yi, domin gudun kada ya fito ya fadi ‘yancin sa a kama shi. Watakila idan an kama mutum kamar yadda aka yi wa wani kwanan nan, to ka ga sai ma an gama zaben sannan a sake shi.

“Ga shi kuma ana bai wa ‘yan sanda damammakin karya doka yadda suka ga dama, ta yadda ba za su bada sararin kowa ya zabi wanda ya ke so cikin kwanciyar hankali ba. Irin wannan yanayin ne ake ciki a yanzu.” Inji Saraki.

BATUN RASHIN HADA-HADAR KUDADE A LOKACIN KAMFEN

“Ina ganin yanayin daukar dawainiyar kamfen din ne ya bambanta a yanzu. Ka ga idan ka dauki bangaren hukumomin gwamnati, su na bi suna takure bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade. Idan da za ka je yanzu ka yi wa manyan manajojin bankuna magana, za su ce maka a takure su ke, an sa musu ido.

“Ana cin-dunduniyar su ta hanyar tirsasa su su aika wa hukuma sunayen wadanda suka ciri kudade. Ka ga a baya kuwa ba a yi wa mutane wannan kwalailaitar.

“Abin da mu ke ji da gani a yanzu dai kam, zan iya ce maka ba haka ingantacciyar dimokradiyya ke tafiya ba. Muddin ana bin cibiyoyin bankuna ana takure su, to su ma zaunawa kawai za su yi su zuba ido. Saboda sun ga an shigo musu da sabon salon da ba dimokradiyya ba ce.

ZARGIN WASU GWAMNONIN PDP NA DA MATSALA DA JAM’IYYA

Saraki ya ce babu wata matsala, kawai duk farfaganda ce ake yi. Ya ce da farko dai ya na sane da cewa akwai ‘yar tirka-tirka, wadda ta faru biyo bayan fidda dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP. Dama a siyasa irin haka na faruwa inji Saraki.

Sai ya ce amma dan lokaci kadan aka shawo kan batun tun ma kafin ya zama matsala, aka dinke, aka amice a tunkari samun nasara kawai, shi ne abin da ke gaban jam’iyyar da mambobin ta.

BATUN KUNCIN RAYUWA A ZAMANIN MULKIN BUHARI

“Idan ka zagaye kasar nan ka na tambayar jama’a shin ka samu wani ingantaccen canjin rayuwa bayan hawan mulkin Buhari fiye da kafin hawan sa? Amsar da za a rika ba ka ita ce har ma gara da bisa ga yanzu.

ALKAWURRAN DA BUHARI YA DAUKA KAFIN ZABE

Saraki ya dauko muhimman alkawurran da Buhari ya yi guda uku, yay i musu filla-fila. Ya yi magana a kan tsaro, tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.

Ya ce a 2015 batun matsalar Boko Haram ake yi, a Arewa maso Gabas. Amma a yau Boko Haram sun kara karfi, su na kwace yankuna daga Najeriya.
Saraki ya yi ikirarin cewa rumbun kididdiga na duniya ya nuna Najeriya ce kasa ta hudu a jerin ksashen da aka fi kashe jama’a sakamakon ta’addanci.

GWAMNATIN APC BA TA YI HOBBASA BA

Saraki ya yi ikirarin cewa gwamnatin APC ba ta yi wani abin a zo a gani ba, domin ta gaza daga abin da aka yi tunani da tsammanin za ta yi wa jama’ar kasar nan.

Da ya juya kan inganta tattalin arziki kuwa, Saraki ya ce APC ta yi alkawarin samar da aikin yi, amma a yanzu matasa sama da milyan 20 sun rasa aikin yi, wasu kuma aikin ne ba su ma samu ba.

“A yau kowa cewa ya ke yi mu ne cibiyar talaucin da mu ke fama da matalauta sama da milyan 80”

BATUN YAKI DA RASHAWA

Saraki y ace ba a taba yin shugaban da gaggan ‘yan wuru-wuru suke kewaye da shi kamar Buhari ba a tarihin Najeriya. A yau sai a kama dan gaban goshin gwamnati, amma a zura ido ana kallon sa, ba a bincike kuma ba a gurfanar da shi, balle a ce an yi masa hukunci.

“Don haka ni ina ganin matsawar shugaba bai iya kama wancan amma ya na iya kama wannan ya kyale wancan, to kimar sa da kallonn nagartar da ake yi masa fa duk ta zube a kasa warwas.

BUHARI DAN HARKALLA NE

An tambayi Saraki ko ya na ganin cewa Buhari dan harkalla da wuru-wuru ne? Sai ya amsa da babbar murya ya ce, kwarai kuwa dan harkalla da wuru-wuru ne. Ya ce domin matsawar za a yi harkalla da wuru-wuru a gaban ka, amma ba za ka iya daukar matakin hukunta wanda ya yi ba, to kai ma mene ne sunan ka?

ZARGINN GWAMNATIN PDP BA TA YI KOMAI CIKINN SHEKARU 16 BA

Saraki ya ce ai duk abin da PDP ta yi ga su nan a fili kowa ya gani. A ta bakin sa, ya ce su ‘yan Najeriya ba shashashu ba ne da za a dode musu ido da rana a ce muhu dare ya yi. Kowa ya gani kuma ya san ayyukan da PDP ta gudanar a cikin shekaru 16 na mulkin ta.

ZARGIN HARKALLA A HARKAR MAN FETUR

Saraki ya ce an tsangwami gwamnatinn Jonathan saboda an yi zargin cewa ana zurara kudade wajen lissafin kudaden tallafin mai.

Ya ce a lokacin gwamnatin Jonathan ta ce ana sayan lita 30 a kullum a Najeriya. Amma ana ganin bai fi a sha lita miliyan 22 ko 23 ba.

“To wannan gwamnatin da ta zo wadda ake yi wa kyakkaywan tunanin cewa za ta rage zurara yawan litar da za ta ce ana sha, daga miliyan 30 ya dawo kasa, maimakon haka sai ma karawa ta yi ta ce wai a yanzu ana shan lita miliyan 50 a kowace rana.”

Saraki ya ce wannan damfara ce, damfarar kuma mai muni matuka.

Share.

game da Author