Maharan da suka yi garkuwa da mahalarta daurin aure su 20 a jihar Katsina, sun yi barazanar kashe su muddun ba a gaggauta biyan su diyyar naira miliyan 20 a jiya Litinin.
An kama mutanen su 20 ne wadanda suka fito daga garin Illela da ke Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina, bayan sun dawo daga halartar daurin aure.
A baya sai da PREMIUM TIMES ta buga labarin garkuwar da aka yi da su tun a ranar 19 Ga Disamba, kan hanyar su ta komawa gda daga taron daurin aure a Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina.
PREMIUM TIMES ta samu rikodin na tattauanawar da aka yi tsakanin daya daga cikin dattawan garin da kuma daya daga cikin masu garkuwa da mutanen.
Ya ce ya bada wa’adin karshen yau Litinin, idan ba a ba su naira milyan 20 ba, to za su kashe mutanen su duka, tunda dangin su ba su kaunar su.
An ce da farko naira milyan 50 suka nema, har aka gangaro kan milyan 30, daga nan kuma a yanzu suka tsaya a kan sai naira milyan 20 ko su kashe mutanen.
Al’ummar kauyen dai sun ce ko naira dubu 100 ba su da ita.
Sun roki a kawo karshen wannan fitina tare kuma da ceto jama’ar su da ke hannun masu satar jama’a.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin.
Discussion about this post