Amfanin Aduwa ko kuma ‘Desert Date’ a jikin mutum

0

Shi dai itacen Aduwa itace ce da ke fidda kwallayen masu matukar amfani a jikin mutum. Aduwa ta yi matukar suna a kasar Arewa musamman a karkara.

Shidai wannan ‘ya’yan aduwa tsotan sa akeyi ko kuma sha. Bayan sha da ake yi akan tatsi mai daga kwalBanda zakin da Aduwa ko kuma Desert Date da turanci kenan take da shi bincike ya nuna cewa tsoson kwallon,man dake cikin ‘ya’yan sannan kuma ita kan ta itacen na da matukar mahimmanci.

Amfanin Aduwa a jikin mutum

1. Aduwa na kawar da cutar asma.

2. Mai fama da atini da zawo zai samu sauki idan ya tsotsi Aduwa

3. Aduwa na kawar da tsutsar ciki.

4. Yana maganin ciwon shawara.

5. Aduwa na maganin farfadiya kuma.

6. Man kwallon Aduwa na rage kiba a jiki, idan ana girka abinci da shi.

7. Yana warkar da ciwo a jiki musamman idan ciwon ya zama gyambo.

8. Man Aduwa na maganin sanyin kashi da kuraje

9. Yana kawar da kumburi

10. Yana kawar da matsalar yin fitsari da jini.

11. Man Aduwa na gyara fatar mutum da hana saurin tsufa.

12. Yana kuma kawar da ciwon bugawan zuciya.

Share.

game da Author