Hukuma na korarin dawo da ’yan matan Najeriya 20,000 da aka yi safara zuwa Mali

0

Hukumar Hana Safarar Jama’a ta Kasa (NAPTIP), ta bayyana kokarin da ta ce ta ke yi, wajen ganin ta gaggauta ceto ‘yan matan Najeriya su kimanin 20,000 da aka yi safarar sau, amma suka makale a kasar Mali.

Shugabar hukumar mai suna Julie Okah-Donli ce ta bayyana haka a cikin wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Abuja.

Ta ce wadannan mata da ke makale a cikin kasar Mali, ba wani aiki ko sana’a suke yi ba sai fa karuwanci kawai.

Ta ce an gano wadannan ‘yan mata ne masu dimbin yawa haka a kasar Mali su na karuwanci, bayan hukumar ta aika da wata tawagar bincike, biyo bayan wani rahoton sirri da hukumar ta samu.

Tawagar ta dawo ta bayyana mana cewa sun gano akwai mata ‘yan Najeriya kimanin 20,000 da ke karuwanci a kasar Mali a sassa daban-daban na kasar.

Cikin watan Disamba ne tawagar ta je ta gudanar da wannan kwakkwaran bincike.

“Mata da dama sun shaida wa tawagar cewa yaudarar su aka yi, aka ce za a kai su ‘Malaisia’, sai suka dauka Malaysia ake nufi.

An ce za a kai su ne domin su yi aiki a otal-otal, gidajen saida abinci, wurin gyaran gashi da kitso da kuma sauran ayyuka masu tasiri.

“Wasu matan ma da kayan makarantar su aka kai su kasar nan, abin da ke nuna cewa sato su aka yi kenan, ba da son ran su suka je kasar ba.”

Shugabar ta NAPTIP ta kuma koka da irin zaman kuncin da ‘yan matan na Najeriya ke yi a Mali.

Ta ce wasu ‘yan matan an saida su ne Naira 600,000 a hannun kawalai, inda aka kai su wurin masu hakar ma’adinai sun a lalata da su ana biya.

“Akalla akwai ‘yan Najeriya miliyan daya da ke zaune a kasar Mali, wadanda 20,000 a cikin su karuwanci suke yi ba da son ran su ba.

“Kuma su na kwana ne a cikin surkukin daji, cikin dakuna marasa galihu, an tsare su ta yadda ba za su iya tserewa ba.

“Idan aka saida yarinya a kan naira 600,000, za a ribanya mata kudin zuwa naira miliyan 1.8 ko naira miliyan biyu. Sai a ce idan ta biya wanda ya saye ta, to ta ‘yantar da kanta kenan, ita ma ta zama babbar Magajiya. Daga nan sai ita ma ta fara tara na ta ‘yan matar ta na jan jari da su.”

Ta ce dalili kenan yaran za su bude karuwanci kadan-gadan domin su kwaci kan su.

Da yawan su na son dawowa Najeriya, kuma kamar yadda Julie ta ce, ana nan ana kokari tsakanin ofishin jakadancin Najerya da na Mali domin ganin an dawo da yaran Najeriya cikin gaggawa.

Share.

game da Author