Biyan kudin ‘Tradermoni’ shashanci ne da wuru-wuru – Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yawon da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ke yi ya na raba naira 10,000 cewa yawon gallafiri ne, shashanci ne kuma wuru-wuru ne da tozarta tsarin aikin ofis.

Wannan bayani ya na cikin wasikar da ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari a fili, kuma ya raba wa manema labarai, a Abeokuta.

Karo na biyu kenan da Obasanjo ya rubuta wa Buhari wasika, ya na mai nuna masa gazawar gwamnatin sa da kuma shi kan sa a matsayin sa na shugaba.

Obasanjo ya ce abin da Osinbajo ke yi cin hanci ne da wuru-wuru, kuma tasirin sa da kimar sa ta mai tsantseni da kyamar harkalla ta zube a kasa. Domin ya bi Yarima domin ya sha dadin kida.

Tsarin Tradermoni tsari ne da gwamnatin Buhari ta shigo da shi domin raba wa ‘yan Najerya milyan biyu jari na naira 10,000 kowanen su.

Osinbajo ne ke gaganiyar raba kudin kusfa-kusfa kuma ya na bi kasuwanni na garuruwa da kuma dandalolin da marasa karfi ke dandazon sayar da kananan kayan amfani mabukata na yau da kullum.

“Wane irin abin kwatagwalci da shasahanci ne wannan, a ce mutumin da ya karanci aikin shari’a da na lauya zai rika bilumbituwa cikin kasuwanni ya na raba wa mutane kudi? Ga ka da ilmin ka, ga ka mataimakin shuagaban kasa, kuma ga shi ka na ikirarin kai malamin addini ne mai tsantseni da zuhudu.

“Mu dai mun mun san ‘yan tireda na gaskiya mabukata su na can cikin kauyuka, kuma su ne ke da bukatar wadannan kudaden idan ma har ya zama dole a bayar din. Ba wai ‘yan tiredar da ke zaune a biranen Lagos da Abuja ba.

“Kuma idan ka bi su da naira 10,000 a matsayin jari, shikenan ka tsaida musu rayuwar su ta dogara kacokan a kan naira 10,000 kenan?

“Ta ya aka bi ana bai wa wasu naira 10,000 ba tare da an bi diddigin milyoyin jama’a da suka rasa ayyukan su a cikin shekaru uku da rabi na wannan mulkin ba?

“Sannan kuma mene ne dangantakar neman sai ka bada lambar katin shaidar rajistar ka da INEC don za a ba ka naira 10,000. Wannan dabara ce ta shirya magudin zabe. Tunda an ce idan na’ura ta ki tantance ka, za ka iya fadin lambar katin ka sai a bar ka ka yi zabe. Shin wadanda ka ba lambar ka ai za su iya zuwa su bayyana ta su yi zabe kawai.”

A matsayin Osinbajo ma mai ilmi ba jahili ba, kamar yadda Obasanjo ya bayyana, ya ce ya kamata ya san wannan kudin da ya ke rabawa ta hanyar sai mutum ya bayar da lambar katin rajistar zabe, to wuru-wuru ne kuma damfara ce, kuma tuggu ne na shirya magudin zabe.

Share.

game da Author