Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa wasu daga cikin wadanda suka yu aiki tare tun a lokacin da yake aikin soja cewa a tsawon gwagwarmayar siyasa da yayi ta fama da, musulmai ‘yan uwan sa da ke kujerun iko ne suka nuna masa kiyayya karara inda Kiristoci suka rungume shi.
” A 2003 da na fara takarar shugabancin Najeriya, bayan zabe mun tafi kotu. A wancan lokaci, kotun wani ne wanda ajin mu daya da shi a makarantar sakandare tare da marigayi Shehu Musa ‘Yar Adua. Lauya na kuma Mike Ahamba, dan kabilar Ibo ne kuma Kirista.
Ahamba ya bayyana wa kotu cewa a kwai wurare da dama da aka yi aringizon kuri’u a zaben kuma ya lissafo su. Ya roki kotu ta san da haka kuma aka amince har ya saka hannu.
” Bayan kotu ta dawo don ci gaba da wannan shari’a, wani kuma da ba musulmi ba sannan dan kabilar Ibo ya sake daga hannu ya na kalubalantar kotu da ta duba korafin da lauya Ahamba ya mika gabanta a zaman farko. Amma kiri-kiri alkalin ya yi watsi da wannan shari’a.
” A rashin gamsuwa muka garzaya kotun koli. A nan ma wanda musulmi ne bafulatani yake shugabantar kotun ya nuna babu abinda ya dame shi game da shari’ar da muka yi watanni 27 muna fafatawa. Bayan lauya na ya karanta korafin mu da ya dauki tsawon awowi 2 da rabi, Alkalin ya kori karar cikin minti 45 kacal.
” A 2007 ma haka akayi alkalin dan Arewa ne kuma musulmi, yayi watsi da karar. A karo na uku ma haka alkalin wanda mutumin Jigawa ne ya yi watsi da karar.
Buhari ya ce wannan shine babban dalilin da ya sa ya ke ganin sassaka addini a cikin abubuwan da muke a kasarnan ba shi da wani alfanu.
Mustapha Jikolo, da shi ne mai tsaron Buhari a lokacin mulkin soja ya jinjina masa bisa irin goyon da yayi musu. Ya ce a dalilin aiki da suka yi da shi sun koyi dabi’u masu kyau da shi ne ya sa suke ta yin gaba a ruwa.
A karshe Buhari ya yi addu’ar neman gafara ga mataimakin sa a lokacin yana mulkin soja, Marigayi Tunde Idiagbon, cewa mutum ne mai kishi da rikon Amana.
” Ko a lokacin da aka yi mini juyin mulki, Idiagbon ya na kasar Saudiyya. An nemi ya dan dakata tukunna sai komai ya lafa amma ya ce ba zai tsaya ba zai dawo, idan kashe ni aka yi shima a kashe shi.” Inji Buhari.
Discussion about this post