Akalla jam’iyyu shida ne suka dunkule wuri daya domin kada gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, na jam’iyyar APC.
Jam’iyyun su ne, PDP, PRP, GPN, ADC,PDM da wasu hasalallun ‘yan jam’iyyar APC.
Babban dalilin da yasa wadannan jam’iyyu suka dunkule waje daya shi don su kada gwamna mai ci, Mohammad Abubakar.
Tsohon ministan ‘Yan sanda Yakubu Lame ya bayyana cewa ba fada suke yi da jam’iyyar APC ba, su gwamnan jihar ne suke fada da kuma sai sun kada shi a zabe mai zuwa.
Haka nan shima Baba Pate na jam’iyyar PRP, ya bayyana cewa rashin tabuka wani abin azo a gani ne da gwamanan jihar bai yi ba a jihar ya sa dole su hadu don fidda mutanen jihar Bauchi daga wannan kangi da rashin iya mulki na gwamnan jihar.
Sai dai kuma a martani da sakataren yada labaran gwamna Abubakar, Abubakar Al-Saddique ya karyata korafe korafen da ake yi kan gwamna Abubakar ya na mai cewa dukkan su borin kunya ce.
Ya ce ba sai ya cika baki ba, su mutanen jihar Bauchi suna sane da abubuwan dake faruwa a jihar, ” Kira kawai nake yi gare su da su tabbata sun yi abin da ya dace Kamar yadda su kayi a 2015 na zaben APC a jihar.
Discussion about this post