RAHOTON MUSAMMAN: Yadda Boko Haram suka maida garin Rann kaburbura

0

PREMIUM TIMES na ci gaba da samun karin sahihan bayanai daga ganau, ba jiyau ba, dangane da yadda wani mummunan hari da Boko Haram suka kai garin Rann ya maida garin tamkar kaburbura.

Dama kuma wannan jarida ta bada labarin yadda sakamakon waharin wanda Boko Haram suka kai a ranar 14 Ga Janairu, ya jefa masu zaune a sansanin gudun hijira har su 76 a cikin halin kunci, saboda jami’an Majalisar Dinkin Duniya da ke gudanar da ayyukan agaji duk tsere daga garin.

PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda mazauna sansanin gudun hijira kusan 76,000 ke cikin halin kaka-ni-ka-yi.

Wani ma’aikacin jiyya mai suna Isa Bwala da ke aiki a karkashin kungiyar jinkai ta Medicines Sans Frontier (MSF), a jihar Barno, ya ce garin Rann da ka sani da dimbin jama’a, yanzu ya zama wata makabarta, tsit ka ke ji, babu kowa.

Bwala ya ce ya je garin ne domin su tantance irin agajin magunguna da mazauna garin ke bukata, kafin ma’aikatan jiyyar su kauce daga garin, ya ce garin ya zama wata fatalwa, shiru ka ke ji, kuma an kacakaca da garin.

Ya bada labarin duk abin da ya gani a cikin mujallar MSF.

“An kona sassa da dama na garin kurmus, kuma lokacin da muka isa garin, wasu wurare sun a cin wuta, hayaki na tashi sama. Wasu wuraren kuma wuta na ta ci.

“Na ci karo da wata mata a lokacin da ta dawo daga wurin rufe gawar mahaifiyar ta da ta ce tsohuwa ce tukuf.

“Ta shaida min an kone ta kurmus a cikin daki, saboda ba ta iya gudun tserad da ran ta.
Shi ma ofishin na kungiyar MSF da dakin ajiyar magungunan da suke kula da masu gudun hijira da su, duk an kona su kurmus.

“Amma mun yi sa’a dukkan ma’aikatan mu sun tsira, wasu sun gudu zuwa cikin kasar Kamaru, tare da mafi yawan al’ummar da suka tsere daga garin.

“Na hangi wani jerin-gwanon jama’a na ta kwarara su na tunkarar cikin kasar Kamaru. Akwai maza da mata da kananan yara, wasu har da jakuna dauke da ‘yan komatsan su da suka rage. Wasu da na yi magana da su, sun ce min zama garin ba na su ba ne.

An kone kasuwar garin uma an sace kayan da ke cikinnkasuwar. Babu sauran wasu kayan abinci a garin. Ko mutum ya tsaya, to babu abin da zai ci.

Duk da cewa ‘yan kalilan na jama’ar da suka rage a Rann kowa ta kan sa ya ke yi, jami’an MSF wadanda dama su liktoci ne ko a ina suke ba tare da wani shamaki ba, sun bayyana cewa su na kokarin kai musu abinci da magunguna.

Yace za a kai abincin ne da magungunan a can cikin karkarar da suka yi mafaka.

Wannan hari da aka kai wa garin Rann da ke cikin Karamar Hukumar Kala Balge, ya sa da yawan wadanda ke zaune garin guduwa zuwa cikin kasar Kamaru. Wasu kuma kamar yadda jami’an jihar suka bayyana, sun tsere Ngala, cikin jihar Barno kusa da Maiduguri.

MSF ta ce kusan masu gudun hijira ne da ke zaune a Rann suka gudu zuwa cikin kamaru, kuma ana sa ran wasu za su ci gaba da yin tururuwa a cikin Kasar,

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa dandazon mutanen da ke yin kaura zuwa cikin Kamaru, ya firgita mahukuntar kasar har suka ba jami’an tsaron umarnin cewa su daina bari ana shiga kasar.

Wannan ne ya sa ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudunn hijara ya ce lada kada Kamaru ta maida masu gudun hijirar cikin Najeriya.

A wannan gari na Rann ne a cikin 2016, sojojin saman Najeriya a bisa kuskure suka jefa bam a sansanin masu gudun hijira, har aka kashe mutane sama da 200.

Share.

game da Author