Jami’in rundunar ‘Operation SHARAN DAJI’ Clement Abiade ya bayyana cewa sojoji sun kashe mahara 58 sannan sun kama daya daga cikin maharan da ransa a dazukan Dumburum da Gando a jihar Zamfara.
Abiade yace sun yi arangama da wadannan mahara ne ranar 20 ga wata Janairu inda a dalilin haka suka rasa rayukan sojoji biyu sannan da rayukan ‘yan kungiyar sa kai biyu.
Ya kuma kara da cewa sun yi watsa-watsa da maboyar mahara 18 inda kuma suka sami nasaran kwato mutane 75 wanda maharan suka yi garkuwa da su.
” Mun kwato bindigogi da wasu makamai da dama da babura 40 daga maboyar maharan’’.
Abiade yace sojoji takwas da ‘yan kungiyar sa kai shida ne suka sami rauni a batakashin inda yuanzu haka suna samun kula a asibiti a Gusau.
A karshe ya ce sun aika da duk mutane 75 din da maharan suka yi garkuwa da su garuruwansu bayan sun yi musu jawabi.