A yau ne mabiya shi’a suka sake fitowa domin gudanar da zanga-zanga domin gwamnatin ta saki shugaban Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.
‘Yan shia’an sun gudanar tattaki daga kasuwar Wuse zuwa gadar Berger a Abuja.
Mabiyan sun fito mazan su da matan su, manya da yara inda suke raye rayen wakoki na kira ga gwamnati da ta saki El-Zakzaky.
Idan ba a manta ba a watan Disambar 2015 ne hukumar tsaro na SSS suka tsare El-Zakzaky da matar sa Zenat a dalilin arangamar da mabiyan sa suka yi da sojojin Najeriya a Zariya.
Har yanzu dai gwamnati na ci gaba da tsare El-Zakzaky bisa umarnin Kotu duk da cewa tun farko kotu ta ba da belin sa.