Hukumar Abinci ta Duniya (FAO) ta koka kan yadda rashin cin abincin dake kara karfin garkuwar jiki ya zama ruwan dare a nahiyar Afrika.
Shugaban hukumar Graziano da Silva ya bayyana haka a taron samun madafa daga matsalolin dake tattare da rashin yin haka da hukumar ta yi a kasar Roma.
Wadannan matsaloli dake tattare da rashin cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki na sa kiba a jiki da kamuwa da wasu cututtuka.
Graziano ya kara da cewa a binciken da aka yi ya nuna cewa mutanen Afrika dake fama da irin wannan matsala sun kai miliyan 672. Sannan kuma yawan irin wadannan mutane zai karu.
Graziano yace ya zama dole hukumar su ta tsara hanyoyin kawar da wadannan matsalolin kafin lokaci ya kure.
Ya ce wayar da kan mutane game da abincin da ya kamata su ci domin inganta garkuwan jikinsu ne mafita.
Discussion about this post