2019: Zan yi wa dan takarar gwamnan Ogun na APC kafar-ungulu a zaben gwamna

0

Gwamnan Jihar Ogun, Ibekunle Amosun na APC, ya yi alkawarin yi wa dan takarar gwamnan jihar sa na jam’iyyar APC, kafar ungulu a zaben gwamna mai zuwa na jihar Ogun.

Amosun, wanda makusancin Shugaba Muhammadu Buhari ne, ya kuma yin alkawarin yin bakin karfin sa domin Buhari ya sake samun nasara.

Ya kuma kara da cewa ba zai bar jam’iyyar APC ba, zai ma yi takarar sanaa a karkashin jam’iyyar APC din a zabe mai zuwa na 2019.

Amosun ya yi wannan jawabi ne a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, a wurin taron masu ruwa da tsaki na dan takarar gwamnan jam’iyyar APM na jihar Ogun, Adekunle Akinlade.

Gwamnan yay i wannan kakkausan furuci ne bayan da ‘yan takarar gwamna su 26 masu goyon bayan sa suka fice daga APC suka koma APM.

Amosun ya ce ya yi matukar kokarin sa wajen ganin ya hana Akinlade da sauran 25 ficewa daga APC, amma abin ya ci tura.

”Ni ba zan hana shi ficewa ba, maimakon haka, zan yi amfani da duk abin da na ke da shi wajen taimaka masa ya samu nasarar zama gwamnan jihar Ogun.

Idan ba a manta ba, Akinlade ne ya ci zaben fidda-gwanin da aka yi tankiya a jihar Ogun, amma sai uwar jam’iyya ta kasa, APC ta canja sunan sa da sunan Dapo Abiodun.

Amosun ya zargi shugaban jam’iyya, Adams Oshiomhole, Segun Osoba da kuma Bola Tinubu da bankara kofa suka fitar da sunan Akinlade, suka maida sunan Abiodun a cikin dakin.

Tun daga lokacin ne aka samu mummunan rikici tsakanin gwamnan jihar Ogun, Amosun da uwar jam’iyyar APC ta kasa.

Share.

game da Author