DOKAR HANA KIWO: Gwamnatin Benuwai ta kwace shanu 105 da ake kiwo ba bisa ka’ida ba

0

Gwamnatin Jihar Benuwai ta bada sanarwar cewa Hukumar Kula da Dabbobi ta Jihar ta kwace wani garken shanu da aka kama ana kiwon su a sarari kusa da Babbar Kwalejin Akawe Torkula da ke Makurdi, babban birnin jihar.

Ta ce shanu ne masu tarin yawa har 105 da kuma tinkiya hudu da aka kama tare da mai kiwon su mai suna Kunje Saija, kamar yadda Kwamandan Kula da Dabbobi na Jihar, Linus Zaki ya tabbatar.

Ya kuma yi karin hasken cewa za a killace shanun wuri daya kamar yadda dokar da ta kafa haramcin yin kiwo a fili ba tare da an killace dabbobi ba a jihar Benuwai ta tanada har tsawon kwanaki bakwai.

Zaki ya ce idan kwanaki bakwai suka cika mai shanun bai je ya biya harajin tara ba, to za a yi gwanjon su ga mai rabo, ita kuma gwamnati ta rike kudin da aka saida shanun a matsayin kudin shiga.

Jihar Benuwai dai ta haramta kiwon dabbobi barkatai a fadin jihar.

Share.

game da Author