Jiya Laraba ne ‘yan sanda suka yi abin da Buhaushe ke kira mai hali ba yan barin halin sa, ko kuma borin-kunya, yayin da suka fitar da sanarwar gaggawa domin su karkatar da hankulan ‘yan Najeriya.
Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa ta musanta tare da karyata labarin da PREMIUM TIMES ta buga wanda ya nuna wasu jami’an ‘yan sandan Mobal su 167 sun arce daga makarantar horaswa ta musamman bayan sun samu labarin cewa da zarar sun kammala atisaye, za a tura ne yaki da Boko Haram.
PREMIUM TIMES ta buga labarin da ya tabbatar da cewa har ma hukumar tsaro ta ‘yan sanda ta buga sunayen su tare da cigiyar su domin a kamo su a humunta su.
Har ila yau kuma wannan jarida ta buga cewa dukkan wadanda suka ari takalmin kare din, babu wanda ya maida bindigar sa ko kakin sa kafin ya tsere.
Sai dai kuma bayan dan lokaci kadan da buga labarin wanda PREMIUM TIMES ta yi, sai Kakakin Rundunar ‘Yan sanda, Jimoh Moshood ya fitar da takarda dauke da bayanan da ya karyata labarin, wanda PREMIUM TIMES ta buga, duk kuwa da cewa akwai hujjoji da suka tabbatar da cewa jami’an tsaro sun buga takarda dauke da sunayen wadanda ake neman din ruwa a jallo, kuma an buga sunayen a PREMIUM TIMES.
Jimoh ya ce ‘yan sanda sun gudanar da bincike kuma sun tabbatar da cewa babu jami’in su ko daya wanda ya tsere, saboda haka labarin ba gaskiya ba ne.
Ya kara da cewa an kirkiri labarin ne kawai don a sare wa ‘yan sanda guiwa daga kokarin da suke yin a dakile ta’addanci a kasar nan.
Jimoh ya ce dukkan sunayen wadanda PREMIUM TIMES ta buga cewa sun gudu, ai tuni duk su na can an tura su Arewa maso Gabas su na gudanar da ayyukan da aka tura su domin su yi.
Jaridar PREMIUM TIMES na nan a kan bakan ta cewa labarin da ta buga gaskiya ne.
Karanta nan ‘Yan sanda 167 da ake nema bayan sun tsere saboda tsoron tunkarar Boko Haram
A yanzu ma wannan labari ya na dauke da ainihin shafin da aka buga tambari da farkon jawabin da ke nuna cewa sun arce, kuma ana neman su.
Baya ga PREMIUM TIMES, wasu jaridu ciki har da PREMIUM TIMES sun ma ruwaito cewa ‘yan sanda 190 ne suka arce, ba 167 kamar yadda PREMIUM TIMES ta buga ba.
Wani babban jami’in ‘yan sanda wanda dama ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da arcewar jami’an, ya kara da cewa fitowar da jami’an ‘yan sanda suka yi suka karyata labarin abin kunya ne da kuma nuni da yadda shugabannin ‘yan sanda ke tozarta kan su a bainar jama’a.
“Abin kunya ne kuma har wani ya fito ya karyata wannan labarin.
“Kai abin dariya ne ma, abin kunya ganin yadda suke yada farfagandar karya ga ‘yan kasa.’’
Wannan jerin sunaye dai an tura su ne ga rundunonin ‘yan sandan mobal, a bisa dukkan alamun da ke nuna cewa an aika da sakonnin ne a inda aka dauko jami’an daga wurare daban-daban.
GA SUNAYEN INDA AKA AIKA DA CIGIYAR ‘YAN SANDA 167
Wuraren sun hada da: Mopol 2, Keffi, Nasarawa; Mopol 3, Enugu, Enugu; Mopol 5, Benin, Edo; Mopol 8, Jos, Jihar Plateau; Mopol 11, Calabar, Jihar Cross River; Mopol 16, Abeokuta, Jihar Ogun; Mopol 17, Akure, Jihar Ondo; Mopol 18, Owerri, Jihar Imo; Mopol 19, Port Harcourt, Jihar Rivers; Mopol 20/22, Ikeja, Jihar Lagos.
Sauran wauraren su ne: Mopol 23, Keffi Street, Ikoyi, Lagos; Mopol 26, Uyo, Jihar Akwa Ibom; Mopol 28, Umuahia, Jihar Abia; Mopol 30, Yenagoa, Jihar Bayelsa, Mopol 31, Asaba, Jihar Delta; Mopol 32, Abakaliki, Jihar Ebonyi; Mopol 35, Dutse, Jihar Jigawa, Mopol 39, Osogbo, Jihar Osun; Mopol 43, Lion Building, Lagos; Mopol 50, Kubwa, Abuja; Mopol 51, Oghara, Jihar Delta, Mopol 54, Onitsha, Jihar Anambra da Mopol 56, Ogoni, Jihar Rivers.
Wani babban jami’an mobal da aka tura wa sakon jerin sunayen wadanda ake cigiyar, da ya samu labarin ‘yan sanda sun karyata labarin da PREMIUM TIMES ta buga, dariya kawai yayi, yace:
“Ai kun dai san halin mutanen na mu, ba abin da ba za su iya fada a cikin bainar jama’a ba, don kawai su fidda kan su daga kunya. Borin-kunya ne kawai suke yi.”
Karanta nan ‘Yan sanda 167 da ake nema bayan sun tsere saboda tsoron tunkarar Boko Haram