Atiku ya nemi a binciki zargin iyalan Buhari na da hannu a mallakar Etisalat da Bankin Keystone

0

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira da babbar murya a gudanar da bincike dangane da zargin cewa iyalan Shugaba Muhammadu Buhari na da babban hannun jari a cikin kamfanin Etisalat Nigeria da kuma Bankin Keystone.

A cikin wata sanarwa da wani kakakin sa mai suna Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce, “ana zargin cewa iyalan Buhari na da jarin da ya kai dala bilyan 2, kwatankwacin naira bilyan 727 a kamfanin Etisalat, wanda a duniya aka kiyasta jarin Etisalat ya kai dala bilyan 20.”

An turo wa PREMIUM TIMES wannan doguwar takarda Shaibu ya fitar a madadin Atiku, inda ta nuna cewa wata majiya da ta karya, ta tabbatar da iyalan Buhari na da makudan kudade a cikin Etisalat da kuma Keystone Bank.

Atiku ya ce iyalan Buhari na da jarin dala bilyan 1.916 a Keystone Bank da kuma wani hannun jari na naira bilyan 3 da suka saya a Bankin Musulunci na Pakistan.

“Na san cewa makon da ya gabata ya dagula wa Buhari lissafi, amma kuma duk da haka ina mai ba shi hakuri dangane da kara dagula masa lissafi da zan yi. Domin batun burgar da ka ke ta yi wai yaki da rashawa, idan abin da ake zargin iyalan ka da shi gaskiya ne, cewa sun shiga harkallar da suka azurta kan su a dare daya, hakan ya saba da ka’idar aikin gwamnati.”

Wannan zargi ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin jam’iyyar APC ta yi shirin yin amfani da bilyoyin kudaden tsarin lamuni ga manoma da Babban Bankin Tarayya, CBN ta bullo da shi, inda aka fake da cewa wai wasu manoma milyan 12 sun tara wa Buhari kudaden kamfen.

Amma Atiku ya gargadi Buhari da kada ma ya sake ya yi amfani da kudin gwamnati ya yi kamfen na zaben 2019 da su.

Musamman Atiku ya ce babu wasu manoman da suka yi wa Buhari karo-karon kudi har naira bilyan 1.7 domin ya yi kamfen. Ya ce shiri ne kawai kuma karyar da ba za a amince da ita ba.

“Shin idan ma an ce manoman milyan 12 suka taimaka wa Buhari da kudaden, kamar yadda su ke so mu yarda, shin hakan bai saba wa dokar Najeriya ta 91(9) ta 2010 ta zabe ba?

Dokar nan fa ta ce kada wani ko wata kungiya ta taimaka da sama da naira milyan 1 ga kowane dan takara.”

Dokar kuma ta tanadi tarar naira milyan daya da daurin shekara daya ga duk wanda ya karya ta.
Atiku ya ce gwamnatin Buhari ta nuna cewa da kudin al’umma ta ke yin gadara da bugun kirjin yin kamfen din zaben 2019 kenan.

Share.

game da Author