Dalilin Majalisar Dattawa na kin amincewa da sabbin mambobin Hukumar EFCC da Buhari ya nada

0

Jiya ne Majalsar Dattawa ta dakatar da amincewa da mambobin Hukumar EFCC da Shugaba Muhammadu Buhari ya aika mata, kuma ya nemi ta amince da su.

Saraki ya bayyana cewa an yarda a dakatar da zaman neman amincewa da mambobin na EFCC har sai an kara tattauna wasu batutuwa da suka shafi majalisa tukunna.

Mambobin na EFCC sun hada da Nda Sule Moses, Lawan Mamman, Najib Galadnci da Adeleke Adebayo.
Tun cikin watan Yuli, 2016 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen, wadanda ya nemi ta amince da su a matsayin mambobi na Hukumar EFCC.

Sai dai kuma an yanke shawarar dakatar da amincewa da su a jiya Talata ne, bayan an tafka zazzafar mahawara a tsakanin dattawan majalisar.

Bayan da shugaban kwamiti a kan EFCC ya gabatar da sunayen domin amincewa, tare da cewa sun cancanta, mutane ne nagari, kwararru kuma masu gogewar iya aiki.

Sai kuma ya kara da cewa wadanda Buhari ya bada sunayen na su, sun fito ne daga Arewa maso Yamma, Arewa Maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yamma.

Sanata Rabiu Kwankwaso dan PDP daga Kano shi da Sanata Barau Jibrin, dan APC daga Kano, suka nemi majalisa ta amince da sunayen.

Sai dai kuma kafin majalisa ta amince da sunayen, sai Sanata Victor Umeh, dan jam’iyyar APGA daga jihar Anambra, ya mike ya yi kaca-kaca da rahoton, ya ce Buhari ya na nuna son kai da wariya da kabilanci, domin babu dan yankin Kudu maso Kudu ko daya a cikin mambobin na EFCC.

Umeh ya ce Magu daga Yankin Arewa maso Gabas ya fito, sakataren EFCC daga Kudu maso Yamma, sannan kuma mambobi biyu daga Arewa.

Daga nan ne aka rika yamutsa gashin baki, har majalisa ta rabu gida biyu, inda wasu na cewa ya kamata a amince da sunayen domin a wuce wurin, wasu kuma na cewa ba su yarda ba, tilas sai an saka sunan dan yankin Kudu maso Gabas tukunna.

Wannan dalili ne ya sa aka dakatar da amincewa da sunayen.

Share.

game da Author