‘Yan bindigar da arce da wata mata mai ciki, mai suna Sumayya Abubakar, sun yi barazanar kashe ta nan da awa 24, idan ba a biya su diyyar naira miliyan 20 kafin su sake ta ba.
A ranar Talata ne suka bada wa’adin awa 48 a cikin maganar da suka yi da mahaifin yarinyar mai suna Abubakar Yusuf.
Domin su tabbatar masa da cewa za su iya kashe Sumayya, maharan sun shaida wa mahaifin na ta cewa sun kashe wani matashi mai suna Surajo, wanda makwaucin Abubakar ne, kuma aka sace su rana daya da Sumayya din.
An sace Sumayya da Umar ne tun cikin watan Oktoba, tare da wasu mutane hudu, daga kauyen Dauran, cikin Karamar Hukumar Zurmi, a Jihar Zamfara.

A ranar Talata, mahaifin Sumayya ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya na tsoron rasa ran ‘yar ta sa.
“Tun daga ranar da aka sace Sumayya har zuwa yau din nan, dukkan mu iyaye da dangin Sumayya ba mu cikin hayyacin mu.
“Irin mawuyacin halin da Sumayya ta ke ciki, dauke da ciki wata biyu a lokacin da aka sace ta, a cikin daji, ga rashin abinci da rashin ruwa, abin takaici da damuwa ne matuka.
“Wadanda suka yi garkuwa da ita su na cewa sai an biya diyyar naira miliyan 150 kafin su sake su. Daga karshe dai sai suka amince da miliyan 30, watau Sumayya naira miliyan 20, shi kuma Surajo naira milyan 10.
“A ranar da aka sako tagwayen nan, gida na ya shiga cikin wani mummunan yanayi, domin abinci ma bai iya ciwo gare ni. Sai da ta kai kadan ya rage zuciya ta ta buga.”
Abubakar ya shaida wa PREMIUM TIMES yadda aka yi kokari aka dan harhada kudade.
‘Na samu na yi magana da masu garkuwar a ranar Talata. Akwai wani dattijo mai suna Lawali Dauda, wanda tamkar uba ya ke a wurin mu. Tun da aka yi garkuwar shi ne ke tataunawa da masu garkuwar.
“Cikin taimakon Allah mun samu mun hada naira miliyan biyar. Daga nai sai Lawali ya kira su ya ce ga naira miliyan 5 an hada, ni zan kawo muku kudin a duk inda ku ke so na kawo muku.
“Amma da suka isa wurin, sai suka rike shi, tsammanin su mahaifin Sumayya ne su ke ta magana da shi kafin ya je wurin su.
“Dan achaba wanda ya kai Lawali wurin da suka ce a same su, ya ce da kunnen sa ya ji suna cewa ya ba su kudi, saboda sun san mahaifin Sumayya attajiri ne a yankin.
Mahaifin Sumayya ya ce sun rike dattijon nan Lawali, su ka ce shi ma ba za su sake shi ba har sai an biya su naira miliyan 50.
“A karshe dai mu ka ci gaba da ja-in-ja har suka ce idan ba mu biya naira miliyan 20 ba, to za su kashe Sumayya da wannan dattijon.
“To a lokacin ne ai suka shaida mana cewa sun kashe Surajo dan makwaubi na, kuma suka rantse cewa idan ba mu biya su naira miliyan 20 nan da kwana biyu ba, to za su kashe Sumayya da dattijo Lawali.
Mahaifin Sumayya ya ce har yau ba su kara samun tallafin ko sisi tun bayan wancan tallafin da suka samu a baya kafin a sako tagwayen ‘yan matan da aka sace a baya ba.
Ya yi kira ga gwamnati da a kai musu daukin gaggawa.
Abubakar ya ce Shugaban Karamar Hukumar Zurmi ba ya yin wani hobbasan taimakawa.
Ya ce ya kuma je har gidan Gwamnatin Jihar Zamafara, inda aka kai shi ofishin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati. Ya ce amma tun daga ranar har yau bai kara jin komai daga gare su ba.
Abin da kawai Shugaban Ma’aikatan ya ce min shi ne, gwamnati na iyar kokarin ganin an sako wadanda ake tsare da su a hannun masu garkuwa da jama’a.
“Amma wai sai ya kara shaida min wai duk wanda ya gano musu inda Sumayya ta ke, to za su ba shi ladar naira milyan 5. Ni kuma na ce masa a’a, to ashe lallai ba son taimakawa ku ke yi ba.”
Ita ma mahaifiyar Sumayya, mai suna Hajiya Hadiza, ta bayyana wa PREMIUM TIMES irin matsananciyar damuwar ta tun bayan sace ta da aka yi.
“A ranar da na samu yin magana da wadanda suka yi garkuwa da Sumayya, sai suka ce min ashe dai mu na son ‘yar mu. Ni kuma na ce musu akwai iyayen da za su ce ba su son ‘yar su?”
Kokarin da PREMIUM TIMES ta yi na magana da Shugaban Karamar Hukumar Zurmi, da Kakakin Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Zamfara da Kakakin Yada Labarai na Gwamnan Zamfara duk ya ci tura.