Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya saka hannu a takardar ‘yarjejeniyar zaman Lafiya a yau Laraba.
Tare da Atiku wajen rakiya, akwai shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus da wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Idan ba a manta a jiya Talata ne shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a takardar yarjejeniyar zaman lafiya. Sai dai Atiku ya bayyana cewa bai halarci taron saka hannun bane saboda kwamitin da ta shirya taron bata gayyace shi ba.
Awoyi kadan bayan wannan korafi da Atiku yayi sai shugaban taron kuma tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar ya karyata ikirarin Atiku.
A wani tattaunawa da PREMIUM TIMES ta yi da shi ya ce, kwamitin sa ta aika wa kowani dan takara takardar gayyata.
” Mu kuwa wane dalili gare mu da za mu ki gayyatar kowa? Wannan sanya hannu kan yarjejeniya ta dukkan jam’iyyun siyasa ce, da nufin amincewa a yi da’a da biyayya ga tsarin da dokoki suka gindaya a lokacin zabe.
To amma idan ma har akwai mishkilar rashinn isar sakon wasikun gayyata ga wasu, ni dai ban sani ba.
Discussion about this post