Buhari na kalubalantar Aisha da masu cewa wasu ke juya shi, su kawo hujjojin su

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu wanda ta ke juya shi a kujerar mulki kamar yadda wasu ke fadi har da matarsa Aisha.

Wannan shine amsar da Buhari ya ba wakilin Muryar Amurka, VOA da ya tambaye shi cewa akwai wannan korafi na cewa wasu ne ke juya shi wanda har uwargidan sa ta fadi haka har sau biyu.

Buhari ya kara da cewa fadin haka da mutane suke yi ya dada tabbatar wa duniya cewa shi cikakken wanda ya yarda ya ba kowa ‘yancin sa ne a karkashin mulkin demokradiyya. Cewa kowa na iya fadin abin da ya ga dama ba tare da muzguna masa ba.

Sai dai Buhari bai tsaya nan ba domin ya kalubalanci duk mai fadin haka gami da matar sa da itama ke irin wannan korafi da su kawo hujjojin su na wai wasu na juya shi ko kuma sukan tilasta masa ya aikata wani aiki ko hidima da karfin tsiya.

Idan ba a manta ba uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari takan yawaita cewa wasu ne ke juya mijin ta inda bashi da sakat sannan bazai iya gudanar da komai ba sai yadda suke so.

Ta taba fadin hakan a hira da tayi da BBC Hausa sannan ta sake cewa a taron mata da aka yi a Abuja cewa wasu mutane uku ne kacal suke cin karen su ba babbaka a kasar nan sannan shi kan sa shugaba Buhari ma suna juya shi ne sai yadda suke so ake yi.

Share.

game da Author