Abin da ya sa Kakakin Majalisar Jiha ke rike da gwamnatin Zamfara a yanzu

0

Bayanai na kara bayyana kan dalilin da ya sa Kakakin Majalisar Jihar Zamfara, Sanusi Rikiji ke rike da mulkin jihar a yanzu, maimakon Mataimakin Gwamna Ibrahim Wakkala.

Rikiji wanda a yanzu shi ne gwamnan riko kasancewa Gwamna Abdulaziz Yari ba ya kasar, shi ne gwamnan ya ba rikon jihar maimakon ya damka ta a hannun Mataimakin Gwamna Wakkala.

Da dadewa ana ta fama da kashe jama’a da kuma yin garkuwa da dama musamman a jihar Zamafara.

A ranar Lahadi da ta gabata ‘yan bindiga sun shiga kauyen Sauna da ke cikin Karamar Hukumar Tsafe, inda suka bindige jama’a da yawa.

Wannan ne ya haifar da mummunar zanga-zanga a jiya Litin a garin Tsafe, inda aka yi kone-konen dukiyar gwamnati da dama, ciki har da hedikwatar karamar hukumar.

Hasalallun sun kuma rika yage fastar hotunan Shugaba Muhammadu Buhari da na gwamana Yari, tare da rera munanan kalaman batunci a kan Buhari, Yari da kuma Ministan Tsaro, Masur Dan-Ali, wanda shi ma dan jihar Zamfara ne?

PREMIUM TIMES ta gano cewa Yari ya fice daga Najeriya, inda tun bayan kwanaki da dama ya tafi Umra a Kasar Saudiyya.

Sai dai kuma ya bar jihar a hannun Rikiji, wanda aka ruwaito cewa an fi ganin gilmawar sa wajen halartar jana’izar wadanda aka karkashe a jihar.

PREMIUM TIMES ta tambayi Kwamishinan Yada labarai na jihar Zamfara, Sanda Danjari, shin ko mene ne dalilin da ya sa gwamna Yari bai bada rikon jihar ga mataimakin sa ba, sai ya ba Kakakin Majaliasar Jihar?

Danjari ya ce: “Dalilin shi ne mataimakin gwamna ya na cikin kungiyar G8, wato ‘yan takarar gwamnan da suka yi adawa da gwamna Yari.

“ Wato akwai bambancin ra’ayin siyasa mai karfi tsakanin gwamna da mataimakin sa, wanda ya hana ya damka masa rikon jihar kafin ya dawo.

“Kai ko ma da shi ma kakakin majalisa ba ya nan., to gwamna zai iya damka rikon jihar a hannun Sakataren Gwamnatin Jiha, maimakon mataimakin gwamna. Kuma wannan ba wani abu ba ne.” Inji Kwamishina Danjari.

Share.

game da Author