Shugaban muryar Najeriya, VON, Osita Okechukwu ya yi kira ga ‘yan uwan sa ‘yan kabilar Ibo da su yi karatun ta natsu sannan su dubi maganar da mataimakin shugaban kasa yayi game da shugabancin kasar nan a 2023 da idon basira su shiga taitayin su.
Idan ba a manta ba mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi kira ga ‘yan uwan sa ‘yan kabilar Yarbawa da su tabbata sun zabi shugaba Muhammadu Buhari a 2019 domin su samu mulki ta dawo bangaren su a 2023.
Shi ko Osita gargadi yayi wa mutanen sa, wato ‘yan kabilar Ibo da su dawo daga rakiyar kiyayyar da suke nuna wa shugaba Buhari su mara masa baya domin samun irin wannan daman da wasu yankin suke nema a gaba.
” Yankin Kudu maso Gabas ne basu taba shugabantar kasar nan ba tun bayan dawowar dimokradiyya a 1999. Idan zamu iya kau da kiyayya mu dawo mu hadu kaf mu mara wa Buhari baya zai iya sa mu yi nasara a karon farko mu shugabanci Najeriya.
” Ina so in tunashe ku cewa Buharin nan fa yana da dandazon masoya da mabiya sama da miliyan 10 a yankin Arewa. Idan muka nuna masa soyayya muka bishi sau da kafa tabbas mutanen sa za su yi mana goma na alheri su mara wa dan kabilar Ibo baya ya shugabanci Najeriya.
” Buhari ya yi mana halacci sannan ya nuna mana soyayya karara. Ku duba irin ayyukan da ake yi a yankunan jihohin Kudu mao Gabas. Saboda haka ina kira gareku da ku farka daga barci mu yi karatun ta natsu a 2019.” Inji Osita Okechukwu.
Discussion about this post