Bankin duniya zai tallafa wa gwamnatin jihar Osun da dala miliyan 20

0

A ranar Laraba ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da cewa gwamnatin jihar Osun za ta samu tallafin dala miliyan 20 daga Bankin duniya domin gyara lalatattun asibitocin dake jihar.

Adewole ya fadi haka ne a Abuja yayin da gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola ya kai masa ziyara.

Adewole ya bayyana cewa Bankin Duniya zai tallafa wa jihar Osun da wadannan kudade ne ta shirin ‘Saving One Million Lives (SOML)’ da ya fara a kwanakin baya.

Bayanai sun nuna cewa kungiyar ‘International Development Association (IDA)’ ce ta tanaji dala 500 domin tallafa wa fannin kiwon lafiya a Najeriya wanda za a raba wa jihohin da ke fama da matsaloli.

A karshe da yake mika godiyar sa bisa wannan kokari gwamnan Oyetola ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta yi amfani da wadannan kudade wajen inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko 332 daga cikin 900 dake jihar.

Share.

game da Author