Kashi 13 bisa 100 na matan da aka yi wa kaciya a Najeriya likitoci ke yi

0

Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun koka kan yadda yi wa mata kaciya ya zama ruwan dare duk da kokarin kawar da shi da ake yi a Najeriya.

Jami’in hukumar kidaya na majalisar dinkin duniya (UNFPA) Eugene Kongnyuy ya fadi haka a taron tsara hanyoyin kawar da wannan matsalar a Najeriya da aka yi a Abuja ranar Laraba.

Kongnyuy yace wani abin takacin shine yadda likitoci suka kwace wannan mummunar sana’ar daga hannun likitocin gargajiyya.

Ya ce bincike ya nuna cewa likitoci sun yi wa mata kashi 13 bisa 100 daga cikin adadin yawan matan da aka yi wa kaciya a kasar nan.

Kongnyuy yace rashin kawar da wannan mummunar al’adar gargajjiyar na cutar da mata ta hanyoyi da dama.

Illolin yi wa mace kaciya sun hada da:

1. Hana mace jin dadin jima’i.

2. Hana haihuwa.

3. Kamuwa da cututtuka irin da sanyi a gaban mace.

4. Kawo zuban jini wajen haihuwa wanda ka iya kawo ajalin mace.

5. Kawo laulayin haila

6. kawo doguwar nakudar haihuwa

Bayan haka ministan kiwon lafiya Isaac Adewole a nashi tsokacin ya ce kokarin kawar da wannan mummunar al’ada na gargajiya n aba su matukar wahala.

Adewole ya ce a yanzu haka kokarin da suke yi ya kara yin wahala ganin cewa likitoci ne suke yi wa mata kaciyan a asibitoci.

” A yanzu haka mutane basa ganin illar yi wa mace kaciya masamman idan likita ko kuma ma’aikaciyar jinya ce ta yi.

A karshe Adewole ya yi kira ga masu fada a ji da kungiyoyin da suka hada kawance da su hada hannu da ma’aikatar kiwon lafiya wajen ganin sun dakile wannan mummunar al’ada daga kasar baki daya.

Share.

game da Author