Jami’in hukumar wayar da kan mutane na kasa (NOA) Zubairu Galadiman Soba ya bayyana cewa har yanzu da akwai katin zabe 500,000 da mutane basu karba ba a jihar Kaduna.
Soba ya fadi haka ne a taron wayar da kan mutane kan mahimmancin zaben shugabanin na gari da aka yi a karamar hukumar Sabongari Zariya ranar Alhamis.
A taron Soba ya yi kira ga duk wadanda basu riga sun karbi katin zaben su ba su gaggauta zuwa domin karbar katin zaben.
Ya ce wadanda suka yi rajista kuma ke da shekaru 18 zuwa sama za su iya karban katunan zaben su a kananan hukumomin su.
Soba ya yi kira ga mutane musamman matasa, ‘yan siyasa da mogoya bayan su kan hada hannu da hukumar kula da aiyukkan zabe don ganin an gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali.
” Ina kira ga matasa da magoya bayan jam’iyyu da su guji aikata aiyukkan ta’addanci sannan su kiyaye dokokin zabe domin ganin an gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali.