Yadda fadan makiyaya da manona ya ci rayukan jama’a da dama a Katsina

0

Fadan makiyaya da manoma da ya barki a kauyen Gora II cikin Karamar Hukumar Safana, ya ci rayuka da dama.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya ruwaito kakakin yada labarai na ‘yan sandan jihar Katsina, Isa Gambo na cewa rikicin ya barke ne a lokacin da wani makiyayi ya banka shanun sa cikin gonar waken wani manomi.

Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa rikicin ya barke ne yayin da makiyayin ya kashe mai gonar a ranar Talata.
Majiyar ta ci gaba da cewa wannan ne ya harzuka dangin mai gonar yin gangamin daukar fansa, inda su ma suka kashe makiyayin.

Wannan majiya dai ta ci gaba da cewa a lokacin da dangin makiyayin suka ji labarin an kashe dan’uwan su, sai suka yi gangami suka dira cikin kauyen Gora II suka rika yin harbin kai mai uwa da wabi, har suka kashe mutane 12.

Isa Gambo ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kwantar da rikicin, kuma an tura da daman su a yankin domin gudun sake barkewar wani sabon rikicin.

Share.

game da Author