Duk Kamfanin da yaki zuwa hutun duk kasa zai gamu da fushin gwamnati

0

Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya gargadi ma’aikatu da makarantu masu zaman kan su cewa dole su rika ba ‘yan Najeriya hakkin su na yin hutun duk kasa idan gwamnati ta bada.

Dambazau ya bayyana cewa dokar kasa ce ta tsara ranakun hutu a kasar nan saboda haka ya zama wa kowani kamfani da wuraren ayyuka su bi wannan doka sau da kafa.

” Idan aka bada hutu kowa ya zauna a gida ya huta.” Haka Dambazau ya ce kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnati tace daga yanzu zata hukunta duk wani kamfanin da ya ki bin wannan doka sau da kafa.

Wasu ma’aikatu, makarantu a Najeriya kan ki zuwa hutu idan gwamnati ta bada. Irin wadannan hutun kuwa sun hada da na Maulidi, Easter, Sallah da dai sauran su.

Share.

game da Author