Dokar kiwon lafiya ta kasa doka ce da a aka shirya domin inganta fannin kiwon lafiya a kasa Najeriya da kuma tsara yadda mutane za su rika samun ingantaccen kula a asibitoci tare da bin doka yadda ya kamata.
Abubuwan da dokar ya ke sun hada da:
1. Samar da nagartattun asibitoci a Najeriya
Dokar ta amince wa ma’aikatar kiwon lafiya ikon kafa kwamitin gudanarwa domin tabbatar cewa duk asibitocin dake kasar da wadanda za a gina daga baya sun cika sharruddan samar da ingantaccen kiwon lafiya a kasa ga kowa da kowa.
Wadannan sharrudda sun hada da inda asibitin yake, ingancin ginin, ingancin kayan aiki, kwarewar ma’aikata, farashin kudin asibiti da dai sauran su.
Sannan wannan kwamitin na da iko rufe duk asibiti ko asibitocin da basu cika wadannan sharudda ba.
2. Bada izinin gina asibitoci na gwamnati da mai zaman kansa.
Bisa dokar kwamitin na da ikon tattance ko kasar na bukatar asibitin gwamnati ko mai zaman kan sa sannan idan ya zama dole a gina guda nawa kasar take bukata.
3. Kare hakin marasa lafiya da hakkokin ma’aikatan kiwon lafiya ga marasa lafiya.
Dokar ta ba mara lafiya izinin samun cikakkun bayanai da bashi kula nagari.
Dokar ta ba marasa lafiya damar kin amincewa da duk kulan da bai gamsu dashi ba.
Mara lafiya ko kuma ‘yan uwan mara lafiya na da ikon shigar da kara a kotu idan asibiti ta maida hankali kan su ko kuma basu
Bisa dokar hukuncin haka shine kotu za ta ci asibitin tarar Naira 100,000 ko kuma zaman kurkuku na tsawon watanni shida.
4. Bada bayanan aiyukka ga duk wanda ke bukata
Bisa dokar, asibitoci basu da damar hana bada bayanan aiyukkan su ga duk wanda ke bukata.
5. Daukan kwararrun ma’aikata da horas da su.
Dokar ta bada izinin daukan kwararrun ma’aikata, horas da su a lokacin da ya kamata sannan da kara wa wadanda suka dace girma.
6. Hana cire wani bangaren jikin mutum batare da izinin sa ba
7. Kafa kwamitin da zai tabbatar wannan kwamitin gudanarwa na aiwatar da aiyukkan su yadda ya kamata.