” PDP da Isah Ashiru mayaudara ne”, Inji Tsohon dantakarar gwamna a PDP, Sani Bello

0

Dan takara gwamna a PDP Sani Bello ya fice daga jam’iyyar PDP a yau lititin.

Sani Bello ya bayyana haka ne a taron manema labari da yayi a garin Kaduna.

Bello ya ce jam’iyyar PDP a jihar ta yaudare shi sannan shi kan sa dan takarar gwamnan jihar Isah Ashiru da ya mara wa baya a zaben fidda gwani ba shi da gaskiya a al’amuran sa.

Sani Bello ya bayyana dalilan da ya sa ya fice daga PDP kamar haka;

” Akwai alkawura da aka yi tsakanina da jam’iyyar PDP cewa idan na janye daga takarar gwamna a lokacin zaben fidda gwani za a saka hannu domin amincewa da wasu bukatu da na nemi ayi sannan a amince min, da a dalilin haka ne na janye wa Isa Ashiru. Sai gashi tun bayan haka jam’iyyar suka yi burus da wannan alkawaru, suka yi watsi da shi kawai abin su.

” Bayan haka kuma ni da kai na nayi binciken wasu daga cikin takardun makarantar Isah Ashiru, kuma na gamsu cewa lallai akwai coge, cuwa-cuwa da kamayamaya a ciki da a dalilin haka yasa ba zan iya ci gaba da bin irin wannan dan takara ba.

” Sannan kuma duk kokarin da na yi tare da wasu ‘ya’yan jam’iyyar domin ganin an warware wannan matsala ya citura domin babu wanda ya waiwaye mu.

Share.

game da Author