SATAR MAGANIN RIGAKAFI: Za a fara kirga kwalaben magani da yawan yara a jihar Sokoto – WHO

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayyana cewa daga yanzu za ta fara kirga kwalaben maganin da aka yi amfani da su wajen yin allurar rigakafi da kuma yawan yaran aka yi wa allurar a karamar hukumar Dange Shuni dake jihar Sokoto.

Jami’in WHO Zayyanu Mu’azu ya sanar da haka da yake ganawa da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Sokoto Ranar Lahadi.

Ya ce bayyana cewa hakan zai taimaka wajen kawar da sace sacen magungunan da wasu ma’aikata kan yi a lokacin da ake aikin rigakafin.

Mu’azu yace WHO ta dauki wannan mataki ne ganin cewa wani ma’aikacin mai suna Babangida Baga ya sace kwalaben maganin rigakafin da ya kamata a yi amfani da su a wannan karamar hukumar.

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Adamu Romo ya bayyana cewa jami’an tsaron sun kama wannan ma’aikaci sannan ana gudanar da bincike a kan sa.

Share.

game da Author