Yawan firgita ga yaro na sa ya kamuwa da cutar hawan jini tun kafin ya manyan ta – Bincike

0

Wani likita a jami’ar Illinois kasar Amurka Jacob Pierce ya bayyana cewa yawan damuwa da firgita ga yara kanana na kawo cututtukan dake kama zuciya kafin su manyanta.

Pierce ya gano haka ne a wani binciken da ya gundanar kan illar da damuwa da yawan firgita ke yi wa kiwon lafiyar yara kanana.

” Sakamakon da na samu ya nuna cewa yaran da suka taso cikin damuwa da yawan firgita kan kamu da hawan jini, shanyewar bangaren jiki da cututtukan dake kama zuciya da kafin su kai matasa akan rasa su.

Ya ce a dalilin haka ne yake kira ga iyaye da masu kula da yaran su da kare su daga yawan fadawa cikin damuwa da abubuwan da zai sa suna firgita a lokacin da suke tasowa.

” Hakan zai kare su daga kamuwa da ire-iren wadannan cututtuka.”

Share.

game da Author