Majalisar Tarayya ta goyi bayan kudirin cire ka’idojin shekarun mai neman aiki

0

Jiya Labara ne Majalisar Tarayya ta amince da sake duba batun cire adadin yawan ko ka’idar shekarun mai neman aiki, domin a sake duba kudirin a karo na biyu.

Wannan na nuni da cewa masu neman aiki sun kusa samun aiki a Ma’aikatun Tarayya, Hukumomi da Bangarorin Ma’aikatun Gwamnati ba tare da nuna banbancin shekarun wanda ake so a dauka ba.

Dan Majalisar Tarayya Sergius Ogun na APC daga Edo ne da kuma Babajimi Benson, dan APC daga Lagos ne suka gabatar da kudirin, inda suka nemi cewa takaita yawan shekarun wanda za a dauka aiki a gwamnati ya na kawo cikas sosai a kasar nan.

Ogun y ace idan aka amince da wannan doka, za a daina daukar aiki ko kuma kin daukar mutum aiki saboda shekarun sa.

A Najeriya ana kin daukar mutum aiki komai kwarewar sa idan adadin shekarun sa bai kai na wanda ake so a dauka ba, ko kuma shekarun sa sun haura na wanda ake so a dauka, duk kuwa da irin kwarewar sa ko basirar sa.

Ya ce dokar za ta fara aiki ne a kan hukumomin gwamnatin tarayya kafin sauran sassan ma’aikatu.
Ya ce wannan hanyar ce kawai za a iya magance yawaitar rashin aiki da matasa da sauran jama’a ke fama da ita a kasar nan.

Ya ce milyoyin zakakuran mutane na nan a kasa ba su da aiki, saboda an rigaya an gindaya sharudda na yawan shekaru ko karancin shekaru na wanda za a dauka aiki.

Benjamin Benson, daya daga cikin wadanda suka gabatar da kudiri, ya ce milyoyin matasa na rasa aiki saboda an tsarma batun bambancin addini, kabila, yare da kuma shekaru ta fam-fam na neman aiki.

Ya ce idan aka kawar da wannan tsari za a samu nasarar kawar da rashin aikin yi a cikin matasan kasar nan da gagarimar nasara.

Share.

game da Author