Ganduje ya maka Ja’afar Ja’afar a Kotu, ya na bukatar a biya shi naira Biliyan 3

0

Duk da nuna shi kiri-kiri a bidiyon da jaridar Daily Nigerian ta saki yana karkacewa ya loda daloli a aljihun sa, gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya maka jaridar Daily Nigerian a kotu cewa ta ci masa mutunci matuka da bidiyon karya.

Lauyan Ganduje, Nuraudden Ayagi ya shigar da wannan kara ne a babban kotu da ke Kano inda yace wannan bidiyo da jaridar ‘Daily Nigerian ta nuna wa duniya ya ci masa mutunci matuka irin wanda ba a taba masa ba.

Lauyan ya ce yana bukatar mawallafin wannan jarida, Ja’afar Ja’afar da ya biya Ganduje naira Biliyan 3 a dalilin cin mutuncin sa da yayi da wadannan bidiyo da ya kira su na karya ne.

Ganduje ya bayyana cewa wadannan Bidiyo na karya ne an shirya su ne domin a ci masa mutunci.

” A matsayina na wanda ya fito daga gidan sarauta sannan gogaggen ma’aikacin gwamnati, wannan abu cin fuska ne matuka gare ni.” Inji Ganduje.

Ayagi ya kara da cewa yana kira ga Kotu da ta tilasta wa mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar da ya bayyana a gaban ta nan da kwanaki 14.

Idan ba’a manta ba Jaridar Daily Nigerian ta bankado wani harkallar daloli in da ya nuna wasu bidiyo dake nuna Ganduje Kuru-kuru yana karkacewa yan zura daloli na cin hanci daga hannun ‘dan kwangila a gidan gwamnati dake Kano.

Ganduje ya karyata hakan inda ya ke ta shelar cewa wannan bidiyo na karya ne. An shirya ne don a ci mutuncin sa.

Share.

game da Author