TAMBAYA: Za a iya yin laya da ganye ko sassaken itace a rataya don wani magani
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad SAW.
Ya halatta Musulumi yayi magani da ganye ko sassake ko dukkan abu mai tsarki. Ana iya rubuta wani bangare na Al-kur’ani ko kyakkyawar addu’a, ko sunayen Allah a ganye ko sassake ko dukkanin wani abin rubutu mai tsarki da tawada mai tsarki.
Sannan ayi amfani da shi wajen magani ko kariya bisa yadda shari’ah ta tsara.
Sharuddan Rubutu Don Magani
1. Tsarki: a rubuta da Alkalami me tsarki, Tawada me tsarki kuma a kan abu me tsarki.
2. Tsafta: Rashin cutarwa ga jikin dan Adam.
3. Rubutun kuma ya kasance rubutu ne me karantuwa ga kowa kuma babu surkulle.
4. Dole ne abinda aka rubuta ya zama Al-kur’ani ko addua, ko sunayen Allah.
Masana sun tabbatar da amfanin yin magani da ayoyin Allah da kuma neman tasirinsa wajen dacewa da samun waraka. Amma fa duk da haka, malamai sunce ba laya bane tafi dacewa da sunnan Manzo SAW. Abinda yafi shi ne:
1. A karanta a tofa a jikin mara lafiyan, ko
2. A karanta a tofa a cikin ruwa, mara lafiyan ya sha ko ya shafa, ko
3. A dafa gurin da ke ciwo a jikin mara lafiya, sannan a karanta, ko
4. A yi hayaki, surace, wanka, ko
5. Ayi rukiya ga mara lafiya.
Rike ko Rataya Laya
Dukkanin Malamai magabata da ‘yan baya sun yi ittifaki akan haramcin rike ko rataya layar da aka yita bada Alkur’ani ba, bada sunayen Allah ba, kuma bada kyakkyawan addu’a ba. Kuma sun dace akan cewa yin hakan shirka ne kuma laifi ne maigirma.
Amma kuma Malaman sun yi sabani a kan Mas’alar rike layar da akayita da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyakkyawar addu’a. Fatawar su ta kasu zuwa gida uku a kan Mas’alar rike ko rataya layar da akayi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyakkyawar addu’a, kamar haka:
1 – Jamhurin Malamai (mafiya rinjaye) sun tafi akan hallacin rike layar da akayi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a, tare da gindaya wasu ka’idojin da za mu ambata.
Mafiya rinjaye daga gawurtattun malamai, kamar malaman duniyar Malikiyya, Shafi’iyya, Hambaliyya, da Hanafiyya duk sun halatta daura layar Alku’ani dogaro da wasu ruwayoyi na manyan magabata kamar Nana-Aisha R.A, Abdullahi Dan Amru R.A da Sa’idu Dan Musayyib da sauransu.
Layar da malaman su ke ganin ya halatta dole ne ya kasan ce:
a) Wani bangare ne na Alkur’ani, sunayen Allah ko kyakkyawar addu’a.
b) Me tsarki, akan abu me tsarki, kuma a rufe ta a cikin abu me tsarki.
c) Ana nufin tabarruki da zikirin da ke cikin layar.
d) Akan yakinin cewa Allah shi ne mai warkarwa, mai karewa ba layarba.
e) Rubutun kuma ya kasance rubutu ne me karantuwa ga kowa babu surkulle a ciki
2) Wasu malaman kuma sun karhanta (sun kyamaci) rike layar da akayi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a. Dogaro ga wasu Nassoshi da ke hani akan hakan. Hadisi ya inganta cewa duk wanda ya rataya laya, to imaninsa ya rataya a gareta.
Manyan magabata kamar Alhassan Albasari da Ibrahim Ibn Muhajir sun kyamaci rike layar da aka yi da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a, ko ingantacen zikiri. Sabo da jin tsoron raunin imani ko fadawa ga shirka.
3) A wani bangaren kuma wasu malaman ne suka haramta rike laya ko wace iri ce.
Malamai kamar su Ibn Bazz, Sheikh Muhammad Ibn Abdulwahhab da riwayar hadisai na Ibn Mas’ud da Imam Ahmad sun haramta rike laya ko wace iri ce sabo da fadin Manzo SAW “ duk wanda ya rataya laya to, ya yi shirka”.
A karshe, Allah ya shiryar da ku, Musulmi zai iya rike laya, matukar layar anyita da Alkur’ani, sunayen Allah ko kyak-kyawar addu’a, kuma tacika sharuddan da ka ambata abaya. Kuma yanada yakinin cewa waraka daga Allah ne, shi ne me karewa, kuma me warkarwa. Sannan ya kudurce a zuciyarsa cewa rike layar domin neman albarkar da ke cikin ayoyin ne, ko sunayen Allan ne ko kuma addu’ar ne. Bugu da kari kuma, wanda zai rike layar, ya kasance mai karfin Imani, ta hanyar da riketa ba zai raunana imanin sa ba, ba zai ji cewa ba layar nada tasirin faruwa ko rashin faruwan wani abu agareshi ba.
Amma fa lalle rashin rike layar yafi alhairi domin kaucewa shirka.
Allah shi ne mafi sani.
Discussion about this post