Ministan Tsare-tsare Udo-Udoma ya yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar nan da su maida hankali wajen yakar matsalar yunwa da ake fama da shi musamman yara kanana.
Ya ce bincike ya nuna cewa yara miliyan 2.5 a Najeriya na fama da matsanancin yunwa sannan illar haka na kawo rauni ga kaifin kwakwalwar yara da hana su girma yadda ya kamata.
Udoma ya kara da cewa ma’aikatar sa ta bude wani asusu na musamman domin taimakawa yaran dake fama da yunwa a kasar nan. A haka kuma yake kira ga gwamnatoci da ma’aikatu da su bi sahun ma’aikatar tsare-tsare domin samun nasarar kau da wannan matsala a kasar nan.
Discussion about this post