Sojoji sun fatattaki Boko Haram, sun kwato muggan makamai

0

Sojojin Najeriya sun bayyana samun nasarar fatattakar wasu ‘yan Boko Haram da suka kai wa wani sansanin sojoji na Bataliya ta 118 hari a jihar Barno.

Sojojin su na sansanin garin Arege ne, da ke cikin Karamar Hukumar Mobbar.

Hukumar Tsaro ta Sojoji ta bayyana a shafin ta na tweeter cewa an fatattaki Boko Haram din ne a ranar Asabar, bayan sun kai harin da misalin karfe biyar na yamma a ranar Juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa sojoji sun kuma samu nasarar kwace motar daukar makamai da daukar dakaru da wasu muggan makamai daga Boko Haram.

An kwace makaman ne kuma an kore su bayan an bude wa juna wuta har tsawon minti 30.

Share.

game da Author