Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saka wa dokar Iko (EO6) hannu da zai hana wasu mashahurai ‘yan Najeriya 50 ficewa daga kasar nan.
A takardar dokar (EO6) Buhari ya umarci ministan shari’a da ya tabbata wadanda sunayen dake kunshe a wannan doka basu fice daga kasar nan ba sannan ana bibiyar asusun ajiyar su.
Ita wannan dokar iko da Buhari ya saka wa hannu ya hana duk wani wanda aka gurfanar da shi a kotu ko kuma a ke bincikar sa da yin harkallar dukiyar kasa da ya kai naira miliyan 50 ko wata kadara mai kwatankwacin haka da kada ya fice daga kasar nan har sai an kammala binciken sa da ake yi.
Bayan haka kuma, za a rika bibiyan asusun ajiyar sa ta banki sau da kafa.
Yanzu dai wasu mashahurai, sannan attajiran Najeriya 50 ne za su fuskanci tsananin wannna doka da Buhari ya saka wa hannu.
A dalilin haka an sanar wa hukumar shige da fice da su tabbata wadannan mutane 50 basu fice daga kasar nan ba sannan ba za a sa ido bisa yadda suke gudanar da hada-hadar kudaden su a bankunan ajiyar su.