Dokar hana fita kasashen waje mulkin kamakarya ne – Inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ta yi fatali da gaba dayan dokar hana wasu da aka ki bayyana sunayen su fta kasashen waje da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa, ta na mai cewa dokar haramtacciya ce kuma ‘Fir’aunaci ne.

A cikin wata takarda da Kakakin Yada Labaran PDP, Kola Ologbondiyan ya saw a hannu, ya ce wannan, “wani sabon salon mulkin Fir’aunaci ne da ake harin kakabawa a kan jam’iyyun adawa da kuma wadanda ake ganin abokan gabar siyasar Muhammadu Buhari ne.

PDP ta ci gaba da cewa Buhari ya yi shiri ne kawai na kuntata wa wasu ‘yan Najeriya masu neman na kan su da manyan ‘yan kasuwa da malaman addini da shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya, wadanda ake ganin cewa ba su goyon bayan sake zaben Buhari a karo na biyu.

PDP ta kara da cewa wannan karfa-karfa ce kuma keta dokar dimokradiyya ce tare da yi wa ‘yan kasa juyin mulki. Wannan ‘yanci inji PDP kuwa ya na nan kunshe a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Jam’iyyar ta ce shiri ne wanda ya kamata duniya ta kalla a matsayin karfa-karfar gwamnatin Buhari wajen takura wa wasu jama’a hana su zirga-zirga da bibiyar su a asirce, ba tare da bin matakin da tsarin mulkin kasar nan ya gindaya ba.

“ Mun fahimci yadda fadar shugaban kasa ta kidime kuma ta gigice tun bayan da ta ji kuma ta gani cewa Atiku Abubakar ne PDP ta tsaida takarar shugaban kasa, kuma fadar ta tsorata da yadda ta ga jama’a na ta murnar tsaida Atiku. To a gefe daya kuma PDP ba za ta yarda sabon salon gwamnatin Buhari na murkushe ‘yan adawa ba.”

A karshe PDP ta ce a zaben 2019 za a kawar da mulkin danniya na gwamnatin Buhari.

Share.

game da Author