Sanata Shehu Sani ya fice daga APC

0

Yanzu dai an rufe kwaryar cece-kucen da taki ci taki cinyewa tsakanin Sanata Shehu Sani da mai ba gwamnan Kaduna shawara kan harkar siyasa Uba Sani.

Jam’iyyar APC ta musanya sunan Shehu Sani da ta ba tikitin kujerar takarar da Uba Sani.

Shehu Sani ya bayyana cewa tunda abin ya zama haka, ya hakura da ci gaba da zama dan jam’iyyar APC daga yau. Yanzu sai dai ba a san ko ina ne zai koma ba.

Idan ba a manta ba, sanata Shehu Sani da gwamnan jihar Kaduna sun saka kafar wando daya ne tun bayan da aka kafa gwamnati a 2015.

Tun daga wancan lokacin aka yi ta kai ruwa rana a tsakanin su inda har ya kai ga jam’iyyar a jihar Kaduna ta kori sanata Shehu Sani.

Sai dai kuma zuwan Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC sai dankon zumunci ya karfafa a tsakanin Shehu Sani da jam’iyyar a sama in da tuni aka yi sanata nadin dan gata.

Yanzu dai ya tabbata Uba Sani ne dan takarar Sanata na Kaduna ta tsakiya shikuma Shehu Sani ya tattara-na-shi- ina-shi ya fice daga jam’iyyar

Share.

game da Author